logo

HAUSA

Majalissar CPPCC za ta fara taron ta na shekara daga gobe Juma’a

2022-03-03 16:23:40 CRI

A gobe Jumaa ne majalissar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ko CPPCC a takaice, za ta fara taron ta na shekara shekara a birnin Beijing. Kakakin majalissar Guo Weimin, wanda ya shaidawa taron manema labarai hakan a Alhamis din nan, ya ce zaman majalissar ta CPPCC zai gudana ne tsakanin ranekun 4 zuwa 10 ga watan nan na Maris, shi ne kuma zama na 5 na majalissar ta 13. (Saminu Hassan)