logo

HAUSA

Kakakin Kasar Sin Ya Soki Demokuradiyyar Amurka Gabanin Taruku Biyu Na Shekara-shekara

2022-03-03 20:34:15 CRI

Mai magana da yawun majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar Sin (CPPCC) Guo Weimin ya soki demokuradiyyar Amurka, yana mai cewa, Amurka na amfani da tsarin demokuradiyya wajen cimma muradunta.

Kakakin ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labaru da aka gudanar a zaman taro na 5 na majalisar CPPCC karo na 13.

A wannan makon ne dai kasar Sin za ta fara taron shekara-shekara na majalisar ta CPPCC da na majalisar wakilan jama'ar kasar wato NPC, dake zama babbar majalisar kafa dokoki.

Guo ya bayyana yayin da yake amsa wata tambaya da aka yi masa kan ko Sin da Amurka suna zawarcin samun bakin fada a ji kan tsarin na demokuradiyya cewa, manufofin Amurka na shirya taron da ake kira wai "Taron demokuradiyya" su ne murkushe wasu, da raba kan duniya da kuma kiyaye martabarta.

Haka kuma, ya yaba da tsarin demokuradiyyar kasar Sin dake mayar da jama’a a gaban komai, da irin rawar da CPPCC ta taka wajen aiwatar da shawarwarin da aka tattauna game da kimiyya da demokiradiyya ta hanyar tuntuba, da sa ido, shiga a dama da kowa, da kuma hadin gwiwa. (Ibrahim)