logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijar ya gana da shugaban kasar

2022-03-02 10:17:08 CRI

A ranar 28 ga wata, jakadan kasar Sin dake janhuriyar Nijar Jiang Feng, ya gana da shugaban kasar Mohamed Bazoum, inda suka tattauna game da batun ci gaban huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Da farko, jakada Jiang ya gabatarwa shugaba Mohamed Bazoum gaisuwar shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma ya jinjinawa huldar hadin gwiwa dake tsakanin kasashen Sin da Nijar, kana ya bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan huldar dake tsakaninta da Nijar, tana kuma fatan yin kokari tare da Nijar, wajen ingiza ci gaban huldarsu bisa babban mataki.

A nasa bangaren kuwa, shugaba Mohamed Bazoum ya gabatar da fatan alherin sa ga takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, haka kuma ya yaba da ci gaban huldar hadin gwiwa dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, inda ya bayyana cewa, kasashen Sin da Nijar abokan hadin gwiwa ne, wadanda ke nunawa juna fahimta da aminci cikin dogon lokaci.

Ya kara da cewa, kasar Sin ta ba da babbar gudummowa ga ci gaban janhuriyar Nijar a fannoni daban daban, musamman ma a bangaren hadin gwiwa, wajen samar da man fetur, kuma kasarsa tana son kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanita da kasar Sin, domin ciyar da huldar gaba yadda ya kamata. 

Hakazalika, jiya Litinin jakada Jiang ya gana da shugaban jaridar “Nijer Inter” ta Nijar Abdullah Moussa, inda sassan biyu suka yi musanyar ra’ayi kan batun game da yadda kasashen nan biyu wato Sin da Nijar suke kara karfafa hadin gwiwa a bangaren watsa labarai. (Jamila)