logo

HAUSA

Biden ya sanar da rufe sararin samaniyar kasarsa ga jiragen Rasha

2022-03-02 14:11:56 CRI

Shugaban Amurka Joe Biden, ya sanar da rufe sararin samaniyar kasar sa ga jiragen saman kasar Rasha. Shugaban ya sanar da hakan ne a jiya Talata, lokacin da yake gabatar da jawabi, gaban hadakar majalissun dokokin kasar, taro irinsa na farko da ya halarta tun bayan darewa shugabancin Amurka, inda ya ce matakin ya biyo bayan matakan soja da Moscow ke dauka ne a kan Ukraine.

Cikin jawabin nasa, Biden ya soki Rasha, tare da jaddada matsayar Amurka na taimakawa Ukraine, to sai dai kuma ya ce sojojin kasarsa ba za su shiga yakin Rasha da Ukraine kai tsaye ba. (Saminu Hassan)