logo

HAUSA

Sin ta gabatar da shirin shekaru 5 game da kula da tsofaffi

2022-03-02 10:39:20 CRI


Mahuntan kasar Sin sun fitar da shirin shekaru 5 game da kula da tsofaffi. Shirin wanda za a aiwatar tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025, zai taimaka wajen inganta kiwon lafiyar tsofaffi.

Mahukuntan kasar sun lura cewa, sama da kaso 78 bisa dari na jimillar tsofaffin kasar na fama da daya daga cututtuka masu tsanani, kuma adadin wadanda ke fama da nakasa sakamakon hakan na ci gaba da karuwa, don haka ne ake tanadar karin hadin gwiwa tsakanin hukumomi masu ruwa da tsaki, da jamiai, da hidimomi da tsare-tsare, domin biyan bukatun tsofaffi.

Shirin ya tanadi aiwatar da matakai na inganta hidimar kandagarki a fannin kiwon lafiyar tsofaffi, da rage ko dakile nakasa, da gushewar tunani sakamakon tsufa. Kaza lika an tanadi karfafan matakai na inganta hidimomi da ake bukata a gidajen tsofaffi, da cibiyoyin dake samar da hidimomi gare su, da fadada amfani da magungunan gargajiya a fannin kula da tsofaffi.    (Saminu)