logo

HAUSA

An Hada Wutar Gasar Wasannin Olympics Ajin Nakasassu Ta Lokacin Sanyi A Beijing

2022-03-02 20:09:28 CRI

Larabar nan ne, aka hada wutar gasar wasannin Olympics ajin nakasassu ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 daga harsunan wuta tara zuwa daya a wurin ibadar aljannar duniya da ke birnin Beijing wato Temple of Heaven.

Daya daga cikin harshen wutan, ya fito ne daga wurin gasar wasannin Olympics ajin nakasassu ta samo asali, wato Stoke Mandeville da ke kasar Birtaniya, daga bisani aka aika da shi zuwa birnin Beijing, don hada shi da sauran harsunan wutar guda 8 da suka fito daga yankunan gasar guda uku na Beijing, da Yanqing da kuma Zhangjiakou.

An dai fara mika wutar nan da nan, bayan da aka hada wutar bisa jigon "Wuta ta sama ta tara," wadda ita ce mafi kololuwar samaniya. Jimillar masu mika wutar 565 ne za su shiga bikin, kashi 21 daga cikinsu kuma na da nakasa. Za kuma a kwashe tsawon kwanaki uku ana gudanar da bikin mika wutar a cikin yankuna uku da za a gudanar da gasar, kafin a shiga da ita cikin filin gandun daji na wasan Olympic a ranar Alhamis da yamma, domin mika ta a cikin tsarin gudanar da gasar.

Za a fara gasar wasannin Olympics ajin nakasassu ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 ne a ranar 4 ga watan Maris, za a kuma kammala a ranar 13 ga watan na Maris. (Ibrahim)