logo

HAUSA

Sin tana son yin kokari tare da kasa da kasa don samun ci gaban tattalin arziki da bunkasuwa mai dorewa

2022-03-02 20:39:30 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a yau cewa, koda yake a shekarar 2021 Sin ta fuskanci kalubale da sauye-sauye da aka samu sakamakon yanayin tattalin arziki a ciki da waje suka haifar, har yanzu tattalin arzikin Sin zai samu ci gaba mai kyau game da nasarori masu tarin yawa.

Wang Wenbin ya bayyana cewa, jimillar tattalin arzikin da Sin ta samu a shekarar 2021 ya kai yuan triliyan 114.4, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 17.7, wanda ya zarce kashi 18 cikin dari bisa na tattalin arzikin duniya, kuma yawansu ya samar da gudummawar bunkasa tattalin arzikin duniya da kashi 25 cikin dari. Yawan GDP na kowane mutum a kasar Sin, ya zarce yuan dubu 80. A fannin jarin waje kuwa, yawan jarin waje da Sin ta yi amfani da shi a shekarar 2021, ya zarce yuan triliyan daya karo na farko, da yawansu ya kai yuan triliyan 1.15, wanda ya karu da kashi 14.9 cikin dari bisa na shekarar 2020, wannan ya shaida cewa, masu zuba jari na kasashen waje, suna da kwarin gwiwa kan damar kasuwanci da yanayin yin ciniki a kasar Sin.

Wang Wenbin ya kara da cewa, Sin tana son kara yin hadin gwiwa tare da bangarori daban daban, don more fasahohin samun ci gaba tare da kasashen duniya, don samar da gudummawa ga farfado da tattalin arzikin duniya, da samun ci gaban tattalin arziki da bunkasuwa mai dorewa. (Zainab)