logo

HAUSA

Ministocin wajen Sin da Ukraine sun tattauna ta wayar tarho kan halin da ake ciki a Ukraine

2022-03-02 10:20:46 CRI

A jiya Talata, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho bisa bukatar da ministan harkokin wajen kasar Ukraine, Dmytro Kuleba ya yi masa.

Kuleba ya yi wa Wang karin bayani game da zagayen farko na tattaunawar da aka gudanar tsakanin Ukraine da Rasha, inda ya bayyana cewa, kawo karshen yakin shi ne babban abin da Ukraine ke baiwa fifiko.

A cewar Kuleba, kofar Ukraine a bude take domin tattaunawa da nufin warware takaddamar dake faruwa, kuma tattaunawar Ukraine da Rasha ta gudana ne bisa gaskiya da kyakkyawar manufa.

Kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa game da batun dake shafar Ukraine, a cewar Kuleba, inda ya bayyana cewa, kasar Ukraine a shirye take ta zurfafa tuntubar juna da bangaren kasar Sin, da kuma neman goyon bayan kasar Sin domin ta kasance mai shiga tsakani don cimma nasarar tsakaita bude wutar rikicin.

Wang ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin kan batun dake shafar Ukraine a bayyane yake, kuma a shirye take a koda yaushe, ya kara da cewa, kasar Sin a ko da yaushe tana tsayawa kan manufar mutunta ikon da dukkan kasashe ke da shi da yankunansu.

Game da halin da ake ciki, kasar Sin ta bukaci bangarorin Ukraine da Rasha da su lalibo bakin zaren warware rikicin ta hanyar tattaunawar sulhu, kana su amince da dukkan muhimman kokarin da kasa da kasa ke yi na neman warware rikicin ta hanyar matakan siyasa, in ji Wang. (Ahmad)