logo

HAUSA

Xi ya fadawa matasa jami'ai da su kasance masu karfin imani, da yin aiki tukuru

2022-03-01 19:25:39 CRI

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci matasa jami'ai da su karfafa akidu da imaninsu, da raya da aiwatar da kyakkyawan hangen nesa kan ayyukansu, su kuma kasance masu yin aiki tukuru kan manufofin da suka shafi jam'iyya da jama'a.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude wani shirin horar da jami'ai matasa da masu matsakaitan shekaru a makarantar kwamitin kolin JKS. (Ibrahim)