logo

HAUSA

Zhang Jun: Ya kamata sassan kasa da kasa su goyi bayan tattaunawar kai tsaye game da batun Ukraine

2022-03-01 11:34:43 CRI

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da su kara azama wajen samar da kyakkyawan yanayi da zai share fagen tattaunawar kai tsaye, game da batun rikicin Ukraine.

Zhang Jun ya ce yanayin da ake ciki a Ukraine na saurin canzawa, kuma ya kai matsayin da Sin, da ma sauran sassa masu ruwa da tsaki ba su yi fata ba.  

Zhang Jun, wanda ke tsokaci yayin zaman gaggawa na babban zauren MDD game da batun Ukraine, ya yi maraba da fara tattaunawa, da shawarwari tsakanin wakilan Rasha da na Ukraine. Yana mai cewa, kamata ya yi Ukraine ta zamo wata gada, ta tattaunawa tsakanin gabashi da yammaci, maimakon cibiyar fito-na-fito tsakanin manyan kasashen duniya.  

Jamiin ya kara da cewa, Sin na goyon bayan kungiyar tarayyar Turai ta EU, da kungiyar tsaro ta NATO, da Rasha, bisa yunkurinsu na hawa teburin shawarwari, duba da muhimmancin wanzar da tsaron bai daya, da martaba damuwar dukkanin sassa game da tsaron kasa, ciki har da na Rasha, da ma batun samar da daidaito, da kafa tsari mai nagarta da dorewa a fannin tsaron nahiyar Turai, ta yadda za a kai ga wanzar da zaman lafiya da daidaito a daukacin yankunan Turai.   (Saminu)