logo

HAUSA

Za a gudanar da zagaye na gaba na tattaunawa game da rikicin Rasha da Ukraine a kan iyakar Belarus da Poland

2022-03-01 10:37:03 CRI

Jagoran tawagar wakilan Rasha a tattaunawar sulhu da ake yi tsakanin Rashan da wakilan Ukraine Mr. Vladimir Medinsky, ya ce za a gudanar da zagaye na gaba, na tattaunawa game da halin da ake ciki, a wani wuri dake kan iyakar Belarus da Poland.

Kamfanin dillancin labarai na Rasha ko RIA Novosti, ya rawaito Medinsky na cewa, abu mafi muhimmanci shi ne an amince a ci gaba da tattaunawa. Jamiin ya kara da cewa, dukkanin wakilan dake halartar tattaunawar, za su koma zuwa yankunan su domin nazartar shawarwarin da aka gabatar yayin zaman farko, kana za su sake haduwa nan da yan kwanaki masu zuwa.

Ya ce yayin zaman farko, an kai ga gabatar da wasu batutuwa, wadanda mai yiwuwa za su taimaka wajen cimma matsaya a nan gaba. (Saminu)