logo

HAUSA

Shoigu: Rasha za ta ci gaba da kai hari a Ukraine har sai ta cimma burinta

2022-03-01 20:29:24 CRI

Ministan tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu ya bayyana a yau Talata a birnin Moscow cewa, kasarsa za ta ci gaba da kaddamar da aikin soji na musamman a kasar Ukraine, har sai an cimma babbar manufar kare kanta daga barazanar da kasashen yamma ke yi mata.

Shoigu ya fada a yayin wani taro da manyan jami’an tsaron kasar suka gudanar ta kafar bidiyo cewa, abu mai muhimmanci a gare mu shi ne, kare kasar Rasha daga barazanar soji daga kasashen yammacin duniya, wadanda ke kokarin yin amfani da al'ummar Ukraine wajen yakar kasarmu.

Ya kara da cewa, sojojin Rasha ba sa mamaye yankin Ukraine, kuma suna daukar dukkan matakan kare rayuka da lafiyar fararen hula.

Shoigu ya ce, ina son in jaddada cewa, ana kai hare-haren ne kawai a kan wuraren da sojoji suke da kuma makamai na musamman.