logo

HAUSA

Wang Yi ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Somaliya

2022-03-01 15:08:01 CRI

Jiya Litinin, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Somaliya Abdi Said, inda ya bayyana cewa, kasarsa tana mai da hankali matuka kan huldar dake tsakanin kasashen biyu wato Sin da Somaliya, kuma za ta ci gaba da samar da tallafi ga kasar Somaliya, yayin da take kokarin raya kasa, kuma kasar Sin za ta ci gaba da nacewa ga manufar rashin tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe, tare kuma da taimakawa kasar dake kahon Afirka, wajen dakile kalubalen kwanciyar hankali, da raya kasa, da kuma gudanar da harkokin kasar.

A nasa bangaren, Abdi Said ya bayyana cewa, Somaliya za ta ci gaba da goyon bayan kasar Sin, kan batutuwan dake shafar babbar moriyar kasar Sin, haka kuma Somaliya tana adawa da cudanyar dake tsakanin yankin Taiwan da Somaliland, saboda hakan na gurgunta ikon mulkin kasar Somaliya, kuma nan gaba Somaliya za ta ci gaba da gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da kasar Sin. (Jamila)