logo

HAUSA

Yanayin kare hakkin dan Adam da Amurka ke ciki ya tsananta

2022-03-01 20:09:25 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi bayani kan rahoton take hakkin dan Adam a Amurka na shekarar 2021 da Sin ta gabatar a kwanakin baya cewa, a cikin rahoton, an yi amfani da al’amura na zahiri da dama da kididdiga don shaida cewa, yanayin kare hakkin dan Adam da kasar Amurka ke ciki ya tsananta.

Wang Wenbin ya yi bayanin cewa, rahoton ya bayyana cewa, a matsayinta na kasa mai tsarin ba da jinya mafi kyau a duniya, yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 da wadanda suka mutu a sakamakon cutar a kasar Amurka, ya kai matsayin farko a duniya. Haka kuma yanayin zaman lafiya da tsaro a kasar Amurka ya tsananta, kana an samu bayanan da suka shafi harbe-harben bindiga 693 a shekarar 2021, karuwar kashi 10.1 cikin dari bisa na shekarar 2020, wadanda suka haddasa mutuwar mutane fiye da dubu 44. Ban da wannan kuma, alkaluman kididdiga sun nuna cewa, mutane fiye da dubu 929 sun mutu a sakamakon yake-yaken ta’addanci da kasar Amurka ta kaddamar a cikin shekaru kimanin 20 da suka gabata.

Wang Wenbin ya kara da cewa, Amurka ta rasa mafakarta ta mai kare hakkin bil Adama, amma ta kara aiwatar da ayyukan diplomasiyya da sunan kare hakkin dan Adam, wannan ya shaida cewa, kasar Amurka tana amfani da ma’auni biyu kan batun kare hakkin dan Adam. (Zainab)