logo

HAUSA

Wang Yi: Sin na fatan sassan kasa da kasa za su kara azama wajen bunkasa kare hakkin bil adama bisa adalci

2022-03-01 10:52:08 CRI

Babban dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su kara azama wajen bunkasa matakan kare hakkin bil adama bisa daidaito da adalci.

Wang Yi, wanda ya yi kiran cikin jawabinsa ta kafar bidiyo, yayin zaman babban taron MDD game da kare hakkin bil adama karo na 49, ya ce martabawa, da kare yancin bil adama jigo ne cikin manyan manufofin JKS, kuma Sin za ta ci gaba da aiki tukuru a wannan fanni, har a kai ga cimma nasarori daidai da yanayi da kuma halin da kasar ke ciki.

Minista Wang ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da shiga a dama da ita a ayyukan kare hakkin bil adama na MDD, ta hanyar gabatar da muryar ta, da ba da gudummawa yadda ya kamata.

Daga nan sai ya yi watsi da zargin da wasu ke yiwa Sin game da batun yankunan Xinjiang da Hong Kong, yana mai bayyana hakan da yunkurin shafawa kasar Sin kashin kaji.

Ya ce "Ba ma bukatar masu nuna kwarewa su yi mana jawabai game da kare hakkin bil adama, kuma ba za mu amince da gungun masu burin yin fito-na-fito da sunan kare hakkin bil adama ba.  (Saminu)