logo

HAUSA

Ukraine ta gabatar da bukatar shiga kungiyar EU

2022-03-01 10:27:35 CRI

Kakakin fadar gwamnatin Ukraine Sergii Nykyforov, ya ce shugaban kasar Volodymyr Zelensky, ya gabatarwa kungiyar tarayyar Turai ta EU da bukatar Ukraine ta zama mambar kungiyar.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafin sa na facebook, Sergii Nykyforov ya ce mika wannan bukata da shugaban Ukraine ya yi a ranar Litinin, wani muhimmin mataki ne a tarihi, kuma Ukraine din na fatan bin hanya ta musamman wajen cimma wannan buri.

A ranar Litinin, shugaba Zelensky ya bukaci kungiyar EU ta yi laakari da hare-haren da Rasha ke kaiwa Ukraine, wajen amincewa da bukatar kasarsa na shiga tarayyar Turai.

A shekarar 2014, lokacin da aka kafa gwamnatin Ukraine mai samun goyon bayan kasashen yamma, Kiev ta yi watsi da wasu manufofin ta na cudanya da sassa daban daban, a kokarin ta na dunkulewa da tarayyar Turai. Tun daga wannan lokaci ne kuma, kasar ke karfafa hadin gwiwa da EU, tare da kyautata alaka da kungiyar tsaro ta NATO, duk da cewa kungiyoyin biyu ba su alkawartawa Kiev din zama mamba ba.  (Saminu)