logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoto Game Da Yadda Amurka Ke Take Hakkin Dan Adam

2022-02-28 19:10:11 CRI

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, yau Litinin ya fitar da rahoton take hakkin dan Adam a Amurka a shekarar 2021.

Rahoton ya bayyana cewa, halin da ake ciki game da batun kare hakkin dan Adam a Amurka, wanda ke kunshe da munanan bayanai, ya kara tabarbarewa a shekarar 2021. Magudin siyasa ya haifar da karuwar mutuwar mutune a sanadiyar annobar COVID-19, yayin da harbe-harben bindiga a kasar ya kai sabon matsayi.

Rahoton ya kara da cewa, tsarin demokuradiyyar karya da ya kai ga take ‘yancin mutane na shiga harkokin siyasa da yadda masu damara ke take doka, ya sanya rayuwa ta yi matukar wahala ga bakin haure da 'yan gudun hijira a Amurka.

Rahoton ya kuma yi nuni da yadda kasar ta Amurka ke ci gaba da nuna wariya ga kananan kabilu, musamman mutanen da suka fito daga Asiya.

A cewar rahoton, ayyukan Amurka na kashin kai sun haifar da sabbin rikice-rikicen jin kai a duniya.(Ibrahim)