logo

HAUSA

Xi Jinping: ya kamata a gaggauta raya manyan kamfanonin Sin dake kan gaba a duniya da kuma horar da kwararru a fannoni daban daban

2022-02-28 20:37:35 CRI

Babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya shugabanci taro na 24 na kwamitin kula da harkokin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ta ketare a dukkan fannoni na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin a yau da yamma, inda ya jaddada cewa, ya kamata a yi kokarin raya tattalin arzikin kasuwanci bisa tsarin gurguzu mai inganci, da ci gaba da kiyaye tattalin arziki mallakar kasa, da gaggauta raya manyan kamfanonin Sin dake kan gaba a duniya wadanda suke samar da kayayyaki masu inganci da yin kirkire-kirkire da kuma dacewa da yanayin da ake ciki yanzu, wadanda za su taka muhimmiyar rawa kan raya kasa ta zamani mai bin tsarin gurguzu da kuma yin kokarin cimma burin raya kasa. Kana ya ce, ya kamata a horar da kwararru a fannoni daban daban bisa yanayin da ake ciki, da kuma horar da kwararru masu nazari da dama don biyan bukatun kasar na yin kirkire-kirkire. (Zainab)