logo

HAUSA

A kullum kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da zaman lafiya da adalci

2022-02-28 18:56:36 CRI

 

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin tana goyon baya tare da karfafa gwiwar duk wani yunkuri na diflomasiyya da zai taimaka wajen yayyata ruwan sanyi kan takaddamar dake tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, ta kuma bukaci a warware rikicin yadda ya kamata.

Wang ya fada a yayin taron manema labaran da aka saba yi yau litinin yayin da aka tambaye shi game da matsayin Sin kan batun Ukraine cewa, kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan tabbatar da zaman lafiya da adalci.

Wang ya kara da cewa, kasar Sin na adawa da yadda bangaren Amurka ke kirkirar bayanan karya da neman bata sunan kasar Sin, a lokacin da yake tsokaci kan rahotannin kafofin watsa labaru na Amurka dake zargin kasar Sin da rawar da take takawa a Ukraine.(Ibrahim)