logo

HAUSA

Kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ya gudanar da bikin murnar sabuwar shekara

2021-12-31 19:08:06 CRI

Kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin ya gudanar da bikin murnar sabuwar shekara_fororder_xi

Yau da safe ne, kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, ya shirya wani biki a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin don murnar sabuwar shekara.

Shugaban kasar Sin, Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a wajen bikin. Inda ya jaddada cewa, a sabuwar shekara, dole ne majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, ta kiyaye tare da inganta tsarin hadin gwiwa tsakanin jam'iyyu, da tuntubar juna ta fuskar siyasa a karkashin jagorancin JKS, da ba da shawarwari game da halin da ake ciki, da kokarin tattara hikima da karfi, domin cimma manufofin kasa da ayyuka da aka tsara. (Ibrahim)