logo

HAUSA

Kasar Sin tana da wani tushen samar da iskar gas da ya kai tan miliyan 10

2021-12-31 15:21:28 CRI

Kasar Sin tana da wani tushen samar da iskar gas da ya kai tan miliyan 10_fororder_211231-yaya-长庆油田

Babban kamfanin hakar mai da iskar gas na Changqing dake arewa maso yammacin kasar Sin, wanda ke karkashin gudanarwar kamfanin mai na kasar Sin CNPC ya bayyana cewa, kasar Sin ta sake bude wani sansanin samar da mai da iskar gas da ya kai nauyin tan miliyan 10. 

Yankin Longdong na rijiyar mai dake karkashin kamfanin Changqing da ke birnin Qingyang na lardin Gansu dake arewa maso yammacin kasar Sin, da yankunan hadin gwiwar raya ikon hako ma'adinai, sun samar da sama da tan miliyan 9.69 na danyen mai da kuma cubic mita miliyan 380 na iskar gas, a bana tare da man da ake hakowa a duk shekara wanda ya haura tan miliyan 10 a karon farko.

Kasar Sin tana da wani tushen samar da iskar gas da ya kai tan miliyan 10_fororder_211231-yaya-长庆油田-hoto2

Shugaban cibiyar binciken fasahar mai da iskar gas na kamfanin Changqing Zhang Kuangsheng ya ce, adadin man da yankin ya tabbatar, ya zarce tan biliyan 3.2 a karshen wannan shekarar.

Birnin Qingyang mai arzikin man fetur, da gawayi da iskar gas, wani muhimmin tushe ne na makamashi a kasar Sin. (Ibrahim Yaya)