logo

HAUSA

Sin za ta ci gaba da kare moriyarta tare da yin hadin gwiwa da sauran sassa wajen kare gaskiya da adalci

2021-12-31 10:47:41 CRI

Sin za ta ci gaba da kare moriyarta tare da yin hadin gwiwa da sauran sassa wajen kare gaskiya da adalci_fororder_211231-Saminu-Sin diplomacy

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ce, a sabuwar shekarar gargajiyar Sin ta Damisa, Sin za ta ci gaba da dora muhimmanci ga kare manyan moriyarta, za ta kuma ci gaba da yin hadin gwiwa da sauran sassan duniya wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaba da irin karsashin irin na Damisa, kuma kasar za ta ingiza manyan nasarori na ci gaban bil adama.

Wan Yi ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da kafar CMG, gabanin shiga sabuwar shekarar 2022, inda ya ce, Sin na adawa da matakan danniya, tana kuma sauke nauyin dake wuyanta a fannin diflomasiyyar kasa da kasa. Yayin da a bana JKS ta cika shakaru 100 da kafuwa, Sin na kara nazartar ci gaban da ta samu. A hannu guda, kasar tare da sauran kasashen duniya, na ci gaba da kalubalantar sassan dake kallon kan su sama da kowa.

Ministan, wanda ya tabo batun yadda Amurka ke sauya matsaya a kan batutuwa da suka shafi diflomasiyya, ya ce muddin Amurka ta yi watsi da manufofin ta na nuna fifiko, alakar ta da Sin na iya sake inganta.

A bangaren tattalin arziki kuwa, Wang ya ce a shekarar 2022, Sin za ta ci gaba da ingiza tasirinta a fannin samar da hajojin masana’antu na bukatun yau da kullum, tare da hada karfi da kasashen yankin ta wajen bunkasa hada hadar tattalin arziki domin cin moriyar juna.

Ya ce Sin ta aiwatar da matakai daban daban na cin moriyar juna ta hanyar kara bude kofa. Cikin shekaru 20 da shigar ta kungiyar cinikayya ta duniya WTO, Sin ta yi rawar gani wajen sauke nauyinta a fannin rage haraji da bude kofar kasuwannin ta.

Wang Yi ya ce a shekarar 2022, Sin za ta yi bukukuwa masu muhimmanci, don gane da zagayowar lokacin kulla dangantakarta da kasashe da dama, za ta yi amfani da lokacin wajen karfafa kawancen gargajiya, da hadin gwiwar ta da sassan kasa da kasa. Game da batun takaddamar zirin Taiwan kuwa, Sin na da tabbacin dinkewa da yankin, matakin da ba wani mahaluki da zai iya dakatar da shi. Kaza lika duk wani yunkuri na balle yankin Taiwan ba zai yi nasara ba.

A fannin yaki da cutar numfashi mai ci gaba da addabar duniya kuwa, ministan harkokin wajen na Sin, ya ce annobar na barazana ga fatan da ake yi na farfadowar tattalin arziki, baya ga matsalolin bin ra’ayin kashin kai da wasu kasashe ke dauka, don haka ya dace sassan kasa da kasa su yi hadin gwiwa domin “fitar da Jaki daga Duma”.

Wang Yi ya ce, ya zuwa ranar 26 da watan Disambar nan, Sin ta samarwa sama da kasashen duniya, da hukumomin kasa da kasa 120, alluran rigakafin cutar COVID-19 sama da biliyan 2, inda ta zamo kan gaba a duniya a wannan fanni. Ya ce Sin ba ta da wata manufa ta siyasa, game da wannan tallafi da take baiwa kasashen duniya, illa dai fatanta na ganin al’ummun duniya sun samu rigakafin da zai ba su kariya daga kamuwa daga cutar. (Saminu Hassan)