logo

HAUSA

Shugaban AU ya bukaci a kai zuciya nesa a Somalia

2021-12-31 10:25:16 CRI

Shugaban AU ya bukaci a kai zuciya nesa a Somalia_fororder_211231-Ahmad 1-Somaliya

Shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika AU, Moussa Faki Mahamat, ya bayyana damuwa game da rikicin siyasar dake ci gaba da ta’azzara a kasar Somalia.

Mahamat ya bukaci a kai zuciya nesa, yayin da ya jaddada muhimmancin cigaba da tattaunawar sulhu a tsakanin shugaban kasa da firaministan kasar domin lalibo bakin zaren warware dambarwar siyasar kasar da ake fuskanta a halin yanzu.

Rikicin siyasa ya kara rincabewa ne a kasar ta gabashin Afrika, bayan sanarwar da shugaban kasar Mohamed Farmajo ya bayar a ranar Litinin na sauke firaministan kasar Mohamed Roble daga mukaminsa bisa zarginsa da hannu wajen aikata rashawa.

Masu sharhi kan al’amurran siyasa sun bayyana cewa, rikicin siyasar da ya kaure a tsakanin manyan shugabannin biyu zai iya haifar da karin jinkirin shirye-shiryen kammala zaben kasar da aka tsara gudanarwa a farkon shekarar 2022. Zaben mambobin majalisar dokokin kasar wanda aka fara a ranar 1 ga watan Nuwamba, an dakatar da shi bayan da aka zabi ’yan majalisa 24 cikin adadin kujerun majalisar dokokin kasar 275.

Tun da farko dai hukumar zaben kasar ta sanya ranar 24 ga watan Disamba a matsayin ranar karshe ta kammala zabukan majalisun dokokin kasar. (Ahmad Fagam)