logo

HAUSA

Adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a Afirka na ci gaba da karuwa

2021-12-31 11:15:14 CRI

Adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a Afirka na ci gaba da karuwa_fororder_hoto

Adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a wasu kasashen Afirka na ci gaba da karuwa, sakamakon yaduwar sabuwar kwayar cutar numfashi ta COVID-19 ta Omicron.

Don haka, wasu kasashen Afirka sun ci gaba da karfafa matakan dakile yaduwar cutar. Gwamnatocin kasashen Kenya, Angola, Jamhuriyyar Congo, da Jamhuriyar Gabon da sauransu, sun bukaci al’ummomi su rika sanya marufin hanci da baki a lokacin da suke shiga ofisoshin hukumomin gwamnatin, kana su rika nuna takardar shaidar samun allurar rigakafi, ko kuma rahoton binciken kwayar cutar COVID-19.

Hukumar kiwon lafiya ta Najeriya ta bayyana cewa, ya zuwa ranar 28 ga wata, kimanin mutum miliyan 10 sun samu allura ta farko a kasar, adadin da ya kai kashi 8.9 bisa dari, na yawan al’ummomin kasar da suka cancanci a yi musu alluran. Kana, mutane sama da miliyan 4.4 sun samu cikakkun allurai, adadin da ya kai kashi 3.9 bisa dari na yawan al’ummomin da suka dace da ka’idar samun allurar.

Shugaba mai kula da harkokin Afirka, a hukumar kiwon lafiyar duniya ta WHO Matshidiso Rebecca Moeti, ta kuma yi kira ga kasashen Afirka, da su gaggauta aikin yi wa al’ummomi alluran, domin ceton rayuka.  (Maryam)