logo

HAUSA

Yadda Aka Dukufa Wajen Raya Kauyen Huawu

2021-12-30 16:36:08 CRI

Yadda Aka Dukufa Wajen Raya Kauyen Huawu_fororder_211230-Maryam-Kauyen Huawu-hoto

A farkon shekarar 2021, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara kauyen Huawu, wani wuri mai nisa dake cikin tsaunin Wuneng na lardin Guizhou na kasar Sin, inda kuma ’yan kalibar Miao suke zama. Kauyen Huawu ya taba fama da kangin talauci mai tsanani, sakamakon yadda tsaunuka suka hana al’ummun su fita waje, da kuma rashin ci gaba a fannin zirga-zirga.

Cikin ’yan shekarun nan, an gina hanyoyin zuwa kauyen Huawu, bisa manufar gwamnatin kasar Sin ta tallafawa al’umma, matakin da ya taimakawa al’ummomin kauyen fita daga kangin talauci.

A halin yanzu kuma, kasar Sin tana cikin muhimmin lokacin raya garuruwa, da kauyuka, bayan ta cimma nasarar kawar da kangin talauci a duk fadin kasar. Shi ya sa, a yayin da shugaba Xi yake ziyarar aiki a kauyen Huawu, ya mai da hankali matuka kan batun raya kauyen.

Fasahar saka ta kabilar Miao, da fasahar rini ta kauyen Hauwu, sun zama fasahohin gargajiyar musamman na wannan wuri, shi ya sa, shugaba Xi ke fatan za a yi amfani da wadannan fasahohi, wajen neman bunkasuwar kauyen Huawu. Ya ce, “Fasahar ta gargajiya ce, wadda ta dace da zamani. A matsayin al’ada, da kuma masana’anta, za ta ba da taimako wajen yada al’adun kasa, al’adun gargajiya, yayin da take taimakawa al’umma wajen fita daga kangin talauci, da kuma neman bunkasar kauyuka da garuruwa.”

Jawabin Xi ya sa kaimi ga mazauniyar kauyen Peng Yi, wadda ta dade tana fatan yada al’adun fasahar saka ta kabilar Miao. Bayan ta sami digiri na biyu a shekarar 2018, ta koma garinta, domin raya fasahar gargajiya, ta hanyar amfani da ilmin da ta koya, da kuma taimakawa mutanen kauyen samun aikin yi. A karshen shekarar 2021 kuma, an ba ta lambar yabo ta “Wakiliyar yada fasahar saka ta kabilar Miao ta kasar Sin”.

A kauyen Huawu, akwai matasa da dama, dake dukufa wajen raya garinsu, kuma a kasar Sin, akwai kauyuka da yawa da suka dukufa wajen neman farfadowarsu kamar yadda kauyen Huawu ya yi. A nan gaba kuma, za su taka muhimmiyar rawa wajen gina kasar Sin, zuwa wata kasa mai wadata.  (Mai Fassarawa: Maryam Yang)