logo

HAUSA

Shekaru 32 ministan harkokin wajen Sin ke ci gaba da fara ziyartar Afirka a kowace shekara

2021-12-30 19:12:49 CRI

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana Alhamis din nan cewa, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai ziyarci kasashen Afirka. Wannan wani ci gaba ne na kyakkyawar al'adar da ministan harkokin wajen kasar Sin ke yi, na fara ziyartar kasashen Afirka a kowace shekara har tsawon shekaru 32, don nuna dadadden zumuncin dake tsakanin sassan biyu.

Ya kuma bayyana cewa, ya kamata Amurka ta jingine yadda take nuna fuska biyu, ta kuma daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin da sunan wai ‘yancin ‘yan jaridu.(Ibrahim)