logo

HAUSA

Xi zai gabatar da sakon murnar sabuwar shekara

2021-12-30 11:15:59 CRI

Da misalin karfe 7 na daren ranar Juma’a 31 ga watan nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai gabatar da sakon sabuwar shekara ta 2022, ta kafar babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), da kuma kafofin yanar gizo. Kana, wasu hanyoyin talabijin na CMG, da gidan rediyon kasar Sin, da shafin intanet na jaridar People's Daily, da shafin intanet na Xinhua, da kuma wasu manyan kafofin watsa labaran kasar Sin, za su fara watsa shirin bisa lokacin da aka tsara. (Maryam)