logo

HAUSA

Kamfanin Huawei zai tallafawa mata da ‘yan matan Afirka da horo a fannin fasahar sadarwa

2021-12-30 10:59:05 CRI

Kamfanin Huawei zai tallafawa mata da ‘yan matan Afirka da horo a fannin fasahar sadarwa_fororder_211230-Huawei-Saminu

Katafaren kamfanin fasahohin sadarwa na kasar Sin Huawei, ya sha alwashin taimakawa rukunonin mata da ’yan matan a kasashen Afirka, da horo, a fannin amfani da na’urori masu kwakwalwa, domin ba su damar cin gajiya a fannonin fasahar sadarwa, da damammakin ayyuka masu nasaba da hakan.

Wata sanarwa da kamfanin na Huawei ya fitar a birnin Nairobin kasar Kenya a jiya Laraba, ta ce shirin na da nufin rage gibin dake tsakanin maza da mata, a fannin ilimin fasahar sadarwa a yankin kudu da saharar Afrika.

Sanarwar ta kara da cewa, karkashin shirin da aka yiwa lakabi da "Shiri domin gobe", kamfanin Huawei zai yi hadin gwiwa da gwamnatocin Afirka, wajen samar da horo a fannonin fasahar sadarwa ga mata da ’yan mata.

Tuni kasashen yankin 14, da suka hada da Kenya, da Uganda, da Ghana, da Malawi, suka rungumi wannan manufa, inda Huawei ya horas da sama da mata 200 a fannonin fasahar sadarwa. Wannan shiri dai ya yi nasara bisa goyon bayan da ya samu daga kasashen Afirka 25, da suka hada Afirka ta kudu, da Kenya, da Najeriya da Ghana. (Saminu Hassan)