logo

HAUSA

Rahoto: Kasar Sin ta samu saurin bunkasuwar fannin masana’antu

2021-12-30 11:08:30 CRI

Rahoto: Kasar Sin ta samu saurin bunkasuwar fannin masana’antu_fororder_211230-China sees surge in manufacturing power development-Ahmad

Wani rahoton da aka wallafa a jiya Laraba ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu bunkasuwa mafi girma na saurin ci gaban fannin masana’antu sama da na kowace kasa a duniya.

A cewar rahoton wanda kwalejin nazarin fasaha ta kasar Sin (CAE) ta fidda ya nuna cewa, kasar Sin ita ce kasar da ta fi kowace kasa a duniya samun saurin bunkasuwar bangaren masana’antu a shekarar 2020.

Baya ga saurin ci gaban da ta samu, sannan kuma karfin bunkasuwar masana’antun ya sake yin la’akari da sauran wasu matakai, da suka hada da inganci da amfani, da kafa tsari mai nagarta da kuma ci gaba mai dorewa. Alkaluman sun nuna matakin ci gaban da bangaren masana’ntun kasar suka samu.

Shan Zhongde, wani masani a kwalejin CAE ya bayyana cewa, tsarin masana’ntun sarrafa kayayyaki na kasar yana da cikakken tsari, kuma yana samun cigaba daga matsakaicin mataki zuwa matakin koli, yayin da ake cigaba da kara samun ingantuwar al’amurra a yin takara. (Ahmad)