logo

HAUSA

Kasuwanci tsakanin Sin da kasashen RCEP ya kusan kaiwa Yuan triliyan 11 a watanni 11 na farkon bana

2021-12-30 11:01:00 CRI

Kasuwanci tsakanin Sin da kasashen RCEP ya kusan kaiwa Yuan triliyan 11 a watanni 11 na farkon bana_fororder_211230-Trade between China and other RCEP members nears 1

Hukumar kwastam ta kasar Sin ta sanar cewa, hada-hadar cinikayya na shige da fici a tsakanin kasar Sin da mambobin kasashen hadin gwiwar raya tattalin arzikin shiyya 14 na (RCEP) ya kai RMB yuan triliyan 10.96 (kwatankwacin dala triliyan 1.72) a watanni 11 na farkon wannan shekara.

Adadin ya kai kashi 31 bisa 100 na jimillar kasuwancin da kasar Sin ta gudanar na kasashen waje, kamar yadda babbar hukumar kwastam ta kasar (GAC) ta sanar a ranar Laraba.

Hukumar GAC ta bayyana cewa, kasar ta dauki matakai da dama don bunkasa harkokin cinikayyarta da sauran mambobin kasashen RCEP, wadanda suka hada da kara fahimtar da kamfanoni game da muhimman matakai dake shafar ayyukan shigi da fici, da daga matsayin fahimtar juna a tsakanin amintattun masu gudanar da harkokin tattalin arziki wato (AEOs), da mambobin kasashen RCEP guda biyar.

Tsarin AEO, wanda hukumar kwastam ta duniya ta kafa, da nufin gudanar da ayyukan tantance kamfanoni ta hanyar shaidun amincewar hukumomin kwastam wanda ya samu cikakkiyar amincewa da kuma dacewa da tsarin shara’a, da samun matsayi mafi daraja.

A cewar GAC, kasar Sin ta riga ta sanya hannu kan yarjejeyar fahimtar juna da tsarin AEO tare da kulla yarjejeniya da kasashe biyar na mambobin RCEP goma wanda aka amince da shi bisa tsarin AEO, kana ana kokarin neman makamanciyar wannan amincewar da sauran kasashen biyar. (Ahmad)