logo

HAUSA

Ma’aikatar wajen kasar Iran ta jinjinawa tattaunawar Vienna

2021-12-29 10:18:55 CRI

Ma’aikatar wajen kasar Iran ta jinjinawa tattaunawar Vienna_fororder_211229-Saminu 1-Iran

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian, ya ce ana ci gaba da samun nasara, a tattaunawar da ake yi a birnin Vienna, game da sake farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015.

Yayin wani taro da ya gudana a jiya Talata, Hossein Amir-Abdollahian, ya ce an rubuta wasu bayanai game da abubuwan da aka amincewa, kuma bangaren Iran na dora muhimmanci kan hakan. Kaza lika sauran sassa ma na maida hankali kan fannonin da aka tantance, da suka kunshi sassan da ake da sabani a kan su.

Jami’in ya kara da cewa, mataimakin shugaban ofishin tsara manufofi na tarayyar Turai EU Enrique Mora ya taka rawar gani wajen tsara tattaunawar da ta kai ga cimma matsayin na yanzu.

Ya ce sauran sassan dake cikin tattaunawar da suka hada da Faransa, da Birtaniya, da Sin da Rasha da Jamus, na maida hankali matuka ga tattaunawar, kuma abu ne mai yiwuwa a kai ga cimma yarjejeniya mai armashi a nan gaba.

Yanzu haka dai, kasar Iran da sauran kasashen 5 na tattaunawa, game da yarjejeniyar nukiliyar Iran din ta shekarar 2015, karkashin zaman hadin gwiwa da aka yiwa lakabi da JCPOA, duk da Amurka ta kauracewa yarjejeniyar a shekarar 2018, karkashin tsohuwar gwamnatin Donald Trump, ta kuma kakabawa Iran sabbin takunkumai.

Rahotanni sun ce a yanzu, Amurka na da hannu a tattaunawar da ake yi a Vienna tun daga watan Afirilu, ko da yake ba ta shiga zaman kai tsaye ba.    (Saminu Hassan)