logo

HAUSA

Ya kamata matakin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje ya taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa

2021-12-29 21:41:04 CRI

Ya kamata matakin fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje ya taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa_fororder_zhang-wei

Yau ne, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya fitar da wata takardar bayani, mai taken "Matakan fitar da kayayyaki na kasar Sin", wadda ta yi bayani dalla-dalla kan tsari da sabbin fasahohin kasar Sin wajen kiyaye zaman lafiya, da ci gaban duniya, da zurfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da kara karfin tattalin arziki da cinikayya na duniya, da ci gaba da bunkasa tattalin arzikin duniya mai inganci.

Mataimakiyar shugaban cibiyar nazarin cinikayya da hadin gwiwar tattalin arzikin kasa da kasa ta ma'aikatar cinikayya Zhang Wei, ta bayyana a cikin wata hira da aka yi da ita cewa, takardar bayanin, ta yi sharhi mai zurfi kan yadda kasar Sin take sarrafa fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, domin taimakawa wajen gina tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa, da kyawawan ayyuka da kokarin da aka yi, na hanyar kula da fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje na kasar Sin, don karfafa tallafi na yau da kullun, da tabbatar da yanayi mai kyau, da samar da fahimtar juna, da muhimmiyar gudummawa.(Ibrahim)