logo

HAUSA

Kakakin ma’aikatar kasuwancin Sin ya yi bayani game da takardar tafiyar da aikin fitar da kayayyaki ta Sin

2021-12-29 15:48:33 CRI

Kakakin ma’aikatar kasuwancin Sin ya yi bayani game da takardar tafiyar da aikin fitar da kayayyaki ta Sin_fororder_hoto

A yau Laraba, kasar Sin ta fidda takardar bayani ta farko game da tafiyar da aikin fitar da kayayyaki. Dangane da wannan takarda, kakakin ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar Sin ya yi bayani da cewa, kasar Sin na fatan kasashen duniya za su kare tsarin kasa da kasa bisa jagorancin MDD, tare da bin dokar kasa da kasa.

Jami’in ya ce a lokacin da manyan kasashen duniya suke aiwatar da nauyin da ke kan su, ya kamata su kare tsaron kasashen duniya a fannin tafiyar da aikin fitar da kayayyaki, domin inganta ayyuka masu nasaba da hakan bisa ka’idar adalci, kuma ba tare da nuna bambanci, da bata ’yancin sauran kasashe a wannan fanni ba. Kana, bai kamata su kafa kariya kan aikin neman bunkasuwa ta hanyar amfani da fasahohin zamani cikin lumana ba, da hadin gwiwar kimiyya da fasaha, da cinikayya bisa doka, da kuma tafiyar da tsarin samar da kayayyaki a tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata.

Kasar Sin tana fatan hadin gwiwar kasashen duniya a fannin tafiyar da aikin fitar da kayayyaki zai kasance bisa adalci, yayin da yake samar da damammaki ga kasa da kasa, da kuma kare moriyar su yadda suke fata.

Cikin shekarun baya bayan nan, kasar Sin ta tsaya tsayin daka, wajen tafiyar da aikin fitar da kayayyaki cikin yanayin tsaro, da kuma kafa sabon tsarin tattalin arziki mai bude kofa ga waje, da kuma ci gaba da kyautata yanayin kasuwanci.

A halin yanzu, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen kara bude kofa ga waje, da yin hadin gwiwa da kasashen duniya domin neman ci gaba tare. Kaza lika kasar Sin za ta ci gaba da inganta tsarin tafiyar da aikin fitar da kayayyaki, domin ba da gudummawarta a fannin kafa tsarin tattalin arzikin kasa da kasa mai bude kofa ga waje.

(Mai Fassarawa: Maryam Yang)