logo

HAUSA

Yake-yake da boyayyun matsalolin tsarin danniya na Amurka

2021-12-29 19:18:13 CRI

Yake-yake da boyayyun matsalolin tsarin danniya na Amurka_fororder_amurka

Yunkurin wani salo na yaki da Amurka ke yi kan kasar Sin, wanda ta shafe shekaru da dama tana yi, ya kara kaimi cikin 'yan shekarun da suka gabata. Kuma daga neman durkusar da kamfanoninta na fasahar kere-kere, da kamfanin sadarwa na Huawei zuwa fara yakin ciniki da fasahar kere-kere. Daga tsoma baki a batun tekun kudancin kasar Sin, da sunan 'yancin zirga-zirga zuwa yada jita-jita game da batun da ya shafi hakkin dan Adam a yankin Xinjiang na Uygur mai cin gashin kansa da kuma yankin Tibet mai cin gashin kansa dukkansu na kasar Sin. Amurka ta tsara dabarun yaki guda daya bayan daya, a wani yunkuri na tada zaune tsaye a kasar Sin, da kassara ci gabanta, da ma tasirinta a harkokin kasa da kasa

Duk da haka, yayin da irin wadannan yake-yake masu yawa da Amurka ta tayar suka taimaka mata wajen ganin bayan abokan hamayyarta, a hannun guda kuma, suna lalata tushen mulkin danniya na Amurkar. Domin duk fa'idar gajeren lokaci da Amurka ta girba, haka nan kuma take yiwa kanta illa na dogon lokaci.(Ibrahim)