logo

HAUSA

Jagororin JKS sun jaddada muhimmancin darajta tarihin kwarin gwiwa da hadin kai da kwazon jam’iyyar

2021-12-29 11:50:11 CRI

Jagororin JKS sun jaddada muhimmancin darajta tarihin kwarin gwiwa da hadin kai da kwazon jam’iyyar_fororder_211229-Saminu 3-JKS

Yayin taron hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar JKS na yini biyu, da aka kammala a jiya Talata, jagororin jam’iyyar sun jaddada muhimmancin darajta ruhin kafuwar jam’iyyar, da martaba tarihin da ta kafa a ayyukan ta, cikin sama da karni guda.

Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, shi ne ya jagotanci taron, inda ya kuma gabatar da muhimmin jawabi.

Yayin taron, wanda ya ba da damar nazartar yanayin da JKS ke ciki, mambobin hukumar siyasar kwamitin kolin jam’iyyar, sun yi amanar cewa, tabbatar da matsayin shugaban kasar Sin, na jagoran kwamitin tsakiya na jam’iyyar, da sauran sassan jagorancin jam’iyyar gaba daya, tare da yadda tunaninsa ya yi tasirin gaske a fagen waiwayar da salon mulkin gurguzu mai halayyar musamman a sabon zamani da ake ciki, sun taimaka wajen ingiza nasarar da Sin ta samu a tarihin ta, da ma yunkurin ta na kara farfadowa.

Mambobin sun kuma amince da cewa, aikin kara inganta jam’iyya ba shi da iyaka, don haka taron ya bukaci a kara azama a fannin gudanar da sauye-sauye, tare da aiwatar da kudurorin nan 8, masu nasaba da inganta aikin jam’iyya, da bin ka’idojin aiwatarwa bisa juriya.

An kuma sanar da za a kira babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 a shekara mai zuwa, kana an bukaci mambobin hukumar siyasar kwamitin kolin JKS, da su jagoranci aiwatar da tsari, da kudurorin da kwamitin tsakiyar JKS ya amince da su.   (Saminu)