logo

HAUSA

Sin: Duniya ta shaida shirye-shirye masu kyau da aka yi game da wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing

2021-12-29 19:24:31 CRI

Sin: Duniya ta shaida shirye-shirye masu kyau da aka yi game da wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing_fororder_olympics-2022

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a Larabar nan cewa, shirye-shiryen wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing sun shiga mataki na karshe, kuma birnin Beijing wanda ya shirya gasannin Olympics har sau biyu, zai gabatar da gasa mai sauki, aminci da ban sha'awa ga duniya.

Zhao Lijian ya yi nuni da cewa, shirye-shiryen wasannin Olympics na lokacin sanyi na birnin Beijing, sun yi kyau matuka, kuma kowa yana iya ganin wannan sakamako a bayyane. A tsawon lokaci, da dama daga cikin 'yan wasa na kasa da kasa, da jama'a daga bangarori daban-daban, da kwamitin shirya gasar wasannin Olympic na kasa da kasa, da sauran kungiyoyin kasa da kasa, duk sun nuna goyon baya da fatansu game da wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing.(Ibrahim)