logo

HAUSA

Bayan kisan Floyd ana zargin ’yan sandan Amurka da ci gaba da hallaka fararen hula

2021-12-29 13:52:59 CRI

Bayan kisan Floyd ana zargin ’yan sandan Amurka da ci gaba da hallaka fararen hula_fororder_211229-Saminu 4-amurka

Wata kungiyar sanya ido mai zaman kanta dake Amurka, mai lakabin “Mapping Police Violence”, ta ce ’yan sandan Amurka sun hallaka mutane 1,646, bayan hallaka matashin nan bakar fata George Floyd a watan Mayun bara, adadin da ya kai kimanin mutum 3 a duk rana.

Wadannan alkaluma dai ba za su yi dadi ga kunnuwan dubban masu zanga zanga, da ’yan rajin kare hakkin al’ummar Amurka ba, musamman ganin yadda suka shafe watanni suna neman a gudanar da sauyi, game da yadda ’yan sanda ke gudanar da ayyukansu bayan kisan Mr. Floyd.

A daya bangaren kuma, masana da dama na ganin alkaluman da kungiyar ta fitar, ba lallai ne su kunshi dukkanin Amurkawa da ’yan sanda ke kashewa a kasar ba. Kaza lika masu fashin baki na ganin adadin wadanda ke rasa rayukansu a kasar, sakamakon amfani da karfi fiye da kima da ’yan sanda ke yi, ya ma dara adadin da kafofin watsa labarai ke bayyanawa.