logo

HAUSA

Kakakin gwamnati: VOA da gwamnatin Amurkar sun hada gwiwa don zubar da kimar kasar Sin

2021-12-29 11:02:20 CRI

Kakakin gwamnati: VOA da gwamnatin Amurkar sun hada gwiwa don zubar da kimar kasar Sin_fororder_211229-Ahmad 2-VOA

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, a lokuta da dama, gidan rediyon muryar Amurka (VOA) ya hada kai da gwamnatin kasar Amurkar wajen siyasantar da al’amurra masu yawa dake shafar kasar Sin da nufin zubar da kima da bata sunan kasar Sin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Zhao Lijian ya yi wannan tsokaci a yayin da yake mayar da martani a rahoton karshen shekara wanda gidan rediyon VOA ya wallafa a baya bayan nan, inda ya yi zargin cewa a shekarar 2021, kasar Sin ta take hakkin dan adam da karya doka a Hong Kong, kuma ta aikata abinda ake kira wai “kisan kiyashi" a Xinjiang.

Zhao yace "A koda yaushe VOA yana yin watsi da gaskiya kuma yana kallon kasar Sin da bakin gilashi mai duhu. Abu ne mai matukar wahala ya gabatar da wani batu mai kyau game da kasar Sin a cikin rahotanninsa." Kakakin ya bayyana cewa, bada jimawa ba, wani tsohon ma’aikacin rediyon VOA ya bayyana cewa, bai taba lura cewa rahotannin da rediyon VOA yake yadawa a kullum sabanin hakikanin abin dake faruwa a kasar Sin ba ne, sai bayan da ya ziyarci kasar Sin.

A cewar Zhao, wannan ma’aikaci ya kuma bayyana cewa, an sallami wasu ma’aikatan rediyon VOA saboda sun bayar da shawarar a kara gabatar da rahotanni masu inganci game da batutuwan dake shafar kasar Sin.

Kakakin ya ce, "Abu ne mai cike da ban mamaki a yi tunanin cewa wasu rukunin mutanen da ba su da hakikanin sha’awar fahimtar batutuwa game da kasar Sin dake aiki a rediyon VOA, suna yin rahoto da kuma yin sharhi game da kasar Sin.”

Ya kara da cewa, dangantakar dake tsakanin rediyon VOA da gwamnatin kasar Amurka kowa ya sani a duk duniya. “Idan har mun fahimci hakan, to ba zai yi mana wahala wajen fahimtar halayyar VOA ba." (Ahmad)