logo

HAUSA

Sin ta samar da karin kashi 19.8 bisa 100 na makalolin kimiyya a 2020

2021-12-28 11:06:06 CRI

Sin ta samar da karin kashi 19.8 bisa 100 na makalolin kimiyya a 2020_fororder_211228-a01-China sees 19

Kasar Sin ta samar da jimillar ingantattun makalolin kimiyya 463,800 a shekarar 2020, inda ya karu da kashi 19.8 bisa 100 idan an kwatanta da adadin na shekarar 2019, kamar yadda wani rahoto ya bayyana a jiya Litinin.

A cewar rahoton, wanda cibiyar nazarin kimiyya da fasahar sadarwa ta zamani dake karkashin ma’aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta gudanar, daga cikin adadin, an wallafa makaloli 216,000 a mujallun kasa da kasa.

Rahoton ya bayyana ingantattun makalolin fasahar a matsayin wadanda aka wallafa a matakan kasa da kasa da kuma mujallun kimiyya na cikin gida a matsayin masu tasiri mai girma da kuma samun karbuwa.

Dangane da fannonin rayuwa, bangaren kula da lafiyar al’umma shi ne ya samu wallafa mafi yawa na makalolin kimiyya da fasahar da aka wallafa a shekarar ta 2020, wanda adadinsu ya kai sama da 71,000, sai bangaren kimiyyar sinadarai wanda ke bi masa baya, sai fannin latironi, sai fasahar sadarwa da na’urori masu sarrafa kansu da kuma fannin nazarin kimiyyar halittu.

Jami’o’i bakwai, da suka hada da jami’ar Shanghai Jiao Tong, da ta Zhejiang, da ta Peking, da jami’ar kimiyya da fasaha ta Huazhong, na daga cikin wadanda ke sahun gaba ta fuskar wallafa ingantattun makalolin kimiyyar, kowace guda daga cikinsu ta wallafa sama da makaloli 5,000, kamar yadda rahoton ya bayyana. (Ahmad)