logo

HAUSA

Antonio Guterres ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su kasance cikin shirin yaki da cututtuka masu yaduwa

2021-12-28 10:50:01 CRI

Antonio Guterres ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su kasance cikin shirin yaki da cututtuka masu yaduwa_fororder_211228-s02-UN chief calls for global solidarity to stop infectious diseases

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga sassan kasa da kasa, da su kasance cikin shirin yaki da cututtuka masu yaduwa. Cikin sakon da ya gabatar ta kafar bidiyo a jiya Litinin, albarkacin “ranar kasancewa cikin shirin yaki da annoba ta duniya” wadda ake bikin ta a duk ranar 27 ga watan Disamba, Antonio Guterres ya ce, samar da tsarin hadin gwiwar duniya a wannan fanni, zai taimaka matuka, wajen baiwa dukkanin kasashe ikon dakile yaduwar cutuka masu bazuwa tun daga tushen su.

Ya ce cutar COVID-19 ta fayyace yadda cuta mai saurin yaduwa kan karade duniya, tare da kassara tsarin kiwon lafiya, da jefa daukacin rayuwar yau da kullum ta bil adama cikin rashin tabbas.

Mr. Guterres ya kara da cewa, cututtuka masu yaduwa na ci gaba da kasancewa masu hadarin gaske ga ko wace kasa, kuma COVID-19 ba za ta zamo ta karshe, cikin cututtukan da bil adama zai sha fama da su ba. Ya ce yayin da duniya ke tunkarar wannan annoba, ya dace a shiryawa tunkarar annoba mai zuwa.

A cewarsa, hakan na nufin zuba jari a fannin sanya ido, da gano alamu tun da wuri, da gaggauta matakan tunkarar kalubale a dukkanin kasashe, musamman wadanda ke da rauni sosai.  (Saminu)