logo

HAUSA

Shirin Sin na samar da isasshen hatsi ya inganta rayuwar al’ummar ta da ma duniya baki daya

2021-12-28 14:08:57 CRI

Shirin Sin na samar da isasshen hatsi ya inganta rayuwar al’ummar ta da ma duniya baki daya_fororder_211228-s03-China

Yayin babban taron shekara shekara na raya karkara da mahukuntan Sin suka kira a kwanan baya, an sake jaddada muhimmancin tabbatar da kasar na samar da isasshen hatsi a ko da yaushe, an kuma yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki da su sauke nauyin dake wuyansu, game da kare filayen noma, da daidaita samar da hatsi yadda ya kamata.

Mahukuntan Sin sun sha alwashin ci gaba da dora muhimmanci kan sha’anin samar da isasshen abinci, cikin ayyukan bunkasa yankunan karkara a shekarar 2022 dake tafe.

Taron ya kuma jaddada ci gaba da maida hankali ga ciyar da daukacin al’ummar Sinawa, a matsayin aiki mai muhimmanci da dukkanin sassan gwamnatocin kasar za su baiwa fifiko. To sai dai kuma, taron ya lura cewa, ciyar da al’ummar Sin da yawan ta ya kai biliyan 1.4, ba aiki ne mai sauki ba.

Tuni dai Sin ta aiwatar da matakai da dama, wadanda suka shafi daukacin sassan bunkasa harkokin noma. Matakan da suka taimaka sosai wajen bunkasa samar da hatsi a kasar. A halin da ake ciki, adadin hatsi da Sin ke samarwa kan dukkanin dan kasa a shekara, ya kai kilogiram sama da 474, adadin da ya dara mizanin kasa da kasa na kilogiram 400. Wannan sakamako ya shaida yadda kasar Sin ta cimma nasarar ninka adadin hatsin da take nomawa, da sama da rubi biyu, daga shekarar 1949 zuwa yanzu, inda a wancan lokaci take samar da adadin kilogiram 209 kan duk dan kasa a shekara.

Bisa wadannan nasarori da kasar ta cimma a fannin samar da isasshen abinci, Sin ta ci gaba da raba fasahohin ta da sauran sassan duniya, wanda kuma hakan ya samu karbuwa matuka ga sassan kasa da kasa.

Ya zuwa yanzu, Sin ta taimaka wajen raba fasahohin inganta noma da yawan su ya kai 1,500 zuwa sassan duniya daban daban, ciki har da dabarun noma tsirrai, da kiwon dabbobi, da tsumin ruwa, da sarrafa albarkatun gona, wanda hakan ya amfani sama da iyalan manoma miliyan 1.5.   (Saminu)