logo

HAUSA

Sin tana adawa da yadda Amurka take fakewa da kasarta

2021-12-28 19:50:06 CRI

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka saba gudanarwa Talatar nan cewa, kasar Sin tana nuna adawa matuka, da matakin da Amurka ta dauka, na ba da labari mara kyau game da kasar Sin, ta hanyar amincewa da kudirin doka, ko yin magudin siyasa wajen fakewa da kasar Sin

A jiya ne, shugaban Amurka Biden ya rattaba hannu kan dokar ba da izinin tsaron kasa na dalar Amurka biliyan 770 na shekarar kasafin kudi ta 2022. Ita dai wannan doka, ta kunshi adadin abubuwa masu alaka da kasar Sin.(Ibrahim)