logo

HAUSA

Shugaban Somali ya kori firaministan kasar bisa zargin rashawa da rikicin zabe

2021-12-28 11:54:34 CRI

Shugaban Somali ya kori firaministan kasar bisa zargin rashawa da rikicin zabe_fororder_211228-a03-Somali president suspends PM over corruption allegations

Shugaban kasar Somaliya Mohamed Farmajo, ya sanar a jiya Litinin cewa, ya sauke firaministan kasar Mohamed Roble, daga mukaminsa bisa zarge-zargen aikata rashawa.

Farmajo ya zargi Roble da hannu wajen aikata rashawa, da kuma yin badakalar filayen gwamnati, cikin wata sanarwa da aka fidda kwana guda bayan zargin da ya yiwa Roble na gazawa wajen tsare tsaren kammala zabukan kasar.

Mataimakin firaministan Mahdi Mohamed Guled, shi ne zai kasance a matsayin firaministan na rikon kwarya, a cewar Farmajo, kana ya yi nuni da cewa, dakatarwar da aka yiwa Roble za ta ci gaba har zuwa lokacin kammala binciken da ake yi masa.

Farmajo ya yi kira ga dukkan jami’an gwamnatin kasar da su guji shiga harkokin badakalar filayen gwamnati, kana su kiyaye dokoki da ka’idojin aikin gwamnati na kasar.

Sanarwar shugaban kasar na zuwa ne ’yan sa’o’i bayan wasu mukamai biyu da Roble ya nada, wanda Farmajo ya yi amanna cewa ya yi hakan ne da niyyar kawo cikas game da binciken da ma’aikatar tsaron kasar ke yi masa.

Masu nazarin al’amurran siyasa na ganin cewa, tsamin dangantakar siyasa a tsakanin manyan shugabannin biyu zai iya haifar da jinkirin kammala zabukan kasar wanda aka tsara gudanarwa a farkon shekarar 2022. A ranar 1 ga watan Nuwamba ne aka fara gudanar da zabukan majalisar dokokin kasar wanda aka dakatar da shi bayan da aka zabi ’yan majalisu 24 daga cikin mambobin majalisun dokokin kasar 275. (Ahmad)