Ya wajaba ’yan siyasar Amurka su gaggauta watsi da mummunan halin su na siyasantar da batun kare hakkin bil adama
2021-12-28 10:18:55 CRI
Wani rahoto da kungiyar manazarta harkokin kare hakkin bil adama ta kasar Sin ta fitar a jiya Litinin, ya soki lamirin yadda ’yan siyasar Amurka suka dukufa, wajen amfani da batun kare hakkin bil adama, wajen cimma manufofin siyasa da mallake duniya.
Rahoton mai taken “Matakin Amurka na siyasantar da batun hakkin bil adama yana rushe ginshikin jagoranci a fannin kare hakkin bil adama”, ya nuna yadda Amurka ke zama barazana ga ci gaban duniya ta fuskar kare hakkin dan adam, tana kuma haifar da karin matsaloli masu alaka da hakan.
Kaza lika rahoton ya fayyace yadda irin wadannan matakai da Amurkar ke dauka, suke tona asirin mummunar rawar da kasar ta taka, a bangaren kare hakkin bil adama a cikin gida, kuma duniya na kara gano gazawar ta wajen kare hakkokin al’ummar duniya.
Rahoton ya yi waiwaye game da abubuwan da suka biyo bayan yakin duniya na II, wadanda ke nuna yadda siyasantar da batun hakkin bil adama ya sabawa manufofi da burikan wanzar da zaman lafiya, da ci gaban al’ummun duniya. Don haka ne rahoton ke ganin muddin wadannan matakai na ’yan siyasar Amurka suka dore, ko shakka babu, ba za a cimma nasarar kawar da mulkin danniya da Amurka ke ikirarin kawarwa ba. (Saminu)