logo

HAUSA

Sin: Amurka ta yi watsi da wajibcin yarjejeniyar kasa da kasa kan sararin samaniya tana haifar da barazana ga rayuwar 'yan sama jannatin Sin

2021-12-28 19:26:34 CRI

Sin: Amurka ta yi watsi da wajibcin yarjejeniyar kasa da kasa kan sararin samaniya tana haifar da barazana ga rayuwar 'yan sama jannatin Sin_fororder_赵立坚

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana Talatar nan, kasar Amurka ta sha bayyana manufar "halayen ya kamata game da sararin samaniya," yayin da ta yi watsi da wajibcin yarjejeniyar kasa da kasa kan sararin samaniya, lamarin da ke zama wata babbar barazana ga rayuwar 'yan sama jannatin kasar Sin. Kuma hakan tamkar nuna fuska biyu ne.

A cewar rahotannin shafin yanar gizon kwamitin MDD mai kula da amfani da sararin samaniya cikin lumana, a ranar 3 ga watan Disamba, zaunanniyar tawagar kasar Sin a MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake birnin Vienna, ta aike da takardar sanarwa ga babban sakataren MDD, tana mai bayyana cewa, tauraron dan-Adam da da kamfanin SpaceX ya harba, ya tunkari tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin sau biyu a wannan shekara, lamarin da ke barazana ga rayuwa da lafiyar 'yan sama jannatin da ke tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin.(Ibrahim)