logo

HAUSA

Yadda Amurka ta siyasantar da hakkin bil Adam ya lalata tushen kula da hakkin bil Adam

2021-12-27 14:04:48 CRI

A yau Litinin, kwamitin nazarin hakkin bil Adam na kasar Sin ya fitar da rahoto mai taken “Yadda Amurka ta siyasantar da hakkin bil Adam ya lalata tushen kula da hakkin bil Adam”. Rahoton ya yi nuni da cewa, domin kiyaye moriyarta a fannin siyasa da ma matsayinta na mafi fada a ji a duniya, Amurka ta yi ta siyasantar da hakkin bil Adam, kuma hakan ya lalata tushen kula da hakkin bil Adam na duniya, wanda kuma ya haifar da babbar barazana ga ci gaban hakkin bil Adam na duniya.

Rahoton ya kuma nuna cewa, in an yi nazari kan sauyawar matsayin kasar Amurka kan hakkin bil Adam a tarihinta, za a gane cewa, ko yadda ta yi oho da hakkin bil Adam a farkon tarihinta, ko kuma yadda daga baya take amfani da batun wajen cimma manufarta, duk sun shaida yadda kasar ke daukar batun hakkin bil Adam a matsayin kayan aikinta na gudanar da gwagwarmayyar siyasa.

Rahoton ya kara da cewa, yadda Amurka take siyasantar da hakkin bil Adam ya fahimtar da al’umma kan cewa, rashin siyasantar da hakkin bil Adam shi ne tushen tabbatar da hakkin bil Adam, kuma magance siyasantar da hakkin bil Adam zai taimaka ga bunkasa hakkin bil Adam a fadin duniya. (Lubabatu)