logo

HAUSA

'Yan sama jannatin Shenzhou-13 sun kammala zagaye na biyu na aikinsu a wajen kumbo

2021-12-27 14:01:53 CRI

‘Yan sama jannatin Shenzhou-13 sun kammala zagaye na biyu na aikinsu a wajen kumbo_fororder_ac4bd11373f082029bd03371bfe058e4aa641be7

Ofishin kula da aikin kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin, ya ce, ya zuwa safiyar yau da misalin karfe 1 saura minti 5, agogon Beijing, bayan da suka shafe kimanin sa’o’i 6 suna gudanar da aiki a wajen kumbo, ’yan sama jannati na kasar Sin na kumbon Shenzhou-13 da suka hada da Zhai Zhigang da Ye Guangfu,sun kammala aikinsu karo na biyu a wajen kumbo, inda suka koma cikin kumbon Tianhe.

Hukumar ta ce wannan aikin, shi ne karo na 4 da aka yi yayin da ake gina tashar bincikrn sararin samaniya ta kasar, inda suka kammala jerin ayyukan da suka hada da daga na’urar daukar hotuna ta C da gwajin aikin wasu sassa na kumbon Tianhe, tare da gwajin fasahohin aiki a wajen kumbo, wanda hakan ya shirya ayyukan da za a gudanar a wajen kumbo nan gaba.

A wata sabuwa, ’yan saman jannati na kumbon Shenzhou-13, za su ci gaba da aikinsu cikin kumbo, inda kuma za su shiga sabuwar shekara ta 2022, hakan nan kuma zai zama karo na farko da ’yan saman jannati na kasar Sin suka shiga sabuwar shekara a sararin samaniya. (Lubabatu)