Ribar masana’antun kasar Sin ta ci gaba da karuwa cikin watanni 11 na farkon bana
2021-12-27 11:52:05 CRI
Alkaluman da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a Litinin din nan sun nuna cewa, ribar da masana’antun kasar Sin ke samu ta ci gaba da karuwa cikin watanni 11 na farkon bana.
Alkaluman sun nuna cewa, masana’antun da ke gudanar da hada hadar cinikayya wadda a shekara ta kai ta kudin kasar a kalla yuan miliyan 20, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 3.14, sun samu karin riba da ta kai kaso 38 bisa dari, tsakanin watan Janairu zuwa Nuwamba, inda suka samu jimillar kudi har RMB yuan tiriliyan 7.98. (Saminu)