logo

HAUSA

Sin: Amurka za ta aika da tawagar jami'an gwamnati zuwa Sin a lokacin wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing

2021-12-27 20:01:30 CRI

Sin: Amurka za ta aika da tawagar jami'an gwamnati zuwa Sin a lokacin wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing_fororder_赵立坚-3

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Litinin din nan cewa, kasar Amurka ta shirya aika wata tawagar jami’an gwamnatinta zuwa kasar Sin, a lokacin gasar wasannin Olympics ta lokaci sanyi ta Beijing, har ma ta gabatar da takardun neman iznin shiga kasar. Kan wannan batu, Zhao ya ce, kasar Sin za ta bi ka'idojin kasa da kasa da suka dace, da dokoki da manufofin da abin ya shafa, na ramawa kura aniyarta.

A baya can, saboda manufar magudin siyasa, Amurka ta ba da umarni tare da aiwatar da abin da ake kira “ba ta tura wakilan diflomasiyya ko jami'anta, don halartar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing" ba tare da an gayyace su ba.(Ibrahim)