logo

HAUSA

An gudanar da babban taron ayyukan raya karkara a Beijing

2021-12-26 20:34:15 CRI

Tsakanin ranakun 25 zuwa 26 ga wannan wata, an gudanar da babban taron ayyukan kyautata ci gaban karkara a birnin Beijing, inda aka yi nazari da kuma tsara ayyukan dake shafar noma, da yankunan karkara, da manoma na shekarar 2022. Gabanin taron, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi. Ya bayyana cewa, domin tinkarar haddura da kalubaloli, akwai bukatar a mayar da hankali kan tsara dabarun game da muhimman bukatun kasa, a tabbatar da dorewar tsarin samar da kayayyaki da rarraba su, kuma a tabbatar da dorewar ci gaban aikin gona da raya yankunan karkara.(Ahmad)